Manyan Ma’aikatan Kwalejin Fasaha Zasu Shiga Yajin Aiki

 

Manyan ma’aikatan kwalejin fasaha (poly) a fadin Najeriya, (SSANIP), sun kaddamar da yajin aikin gargadi a fadin tarayya kan rashin biyan bukatunsu da gwamnatin tarayya tayi.

A ganawar shugabannin kungiyar ma’aikatan, an gargadi gwamnatin tarayya cewa idan bata biya bukatun ma’aikata ba, mambobin kungiyar zasu shiga wani yajin aikin gaba daya.

Shugaban SSANIP na kasa, Philip Ogunsipe, ya ce sama da shekaru 10 kenan ana yarjejeniya kuma har yanzu ba’a cimma matsaya ba.

Philip Ogunsipe, ya ce gwamnatin tarayya na cigaba da yiwa lamarin rikon sakainar kashi, hakan ya sa suka yanke shawarar shiga yajin aikin gargadi na kwanaki 14.

Shugabannin SSANIP na kwalejin fasaha daban-daban a fadin tarayya sun yi amanna da wannan hukunci da uwar kungiyar ta yanke kuma tuni sun kaddamar da yajin aikin.

Daga cikin wadanda suka tabbatar da hakan akwai shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Legas, Oluseye Ero-Philips; shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Ede, Emmanuel Oyeyode; shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Offa, Oyinlola Abdulmajeed; da shugaban SSANIP na kwalejin fasahar Nekede, Christian Ononogo.

naija celebrity news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here