Muna Sane da ƙalubalen da Ake Fuskanta a Wasu Yankuna – Shugaban INEC
Shugaban hukumar zaɓen Najeriya (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya ce hukumar na lura tare da sanya ido game da yadda zaɓe ke gudana a faɗin ƙasar.
Ya ce hukumar ta samu rahotonnin wasu ‘yan matsaloli nan da can, to sai dai hukumar a shirye take wajen magance matsalolin.
A yau ne dai hukumar ke gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin tarayya.
Read Also:
Farfesa Mahmud ya ƙara da cewa burin hukumar shi ne tabbatar da samun sahihi da ingantaccen zaben a ƙasar.
Farfesa Yakubu ya ce wannan shi ne karo na farko da hukumar ke gudanar da zaɓen kamar yadda aka tsara ba tare da ɗage zaɓen ba.
Ya ce ana ci gaba da zaɓe a faɗin ƙasar, kuma na’urar BVAS da ake amfani da ita tana aiki yadda ya kamata a wurare da dama a faɗin kasar.
Ya ce rahotonnin da hukumar ke samu daga ofisoshin hukumar na jihohi da birnin tarayya na nuna cewa ƙorafe-ƙorafen da jama’a ke yi game da aikin na’urar BVAS na ci gaba da raguwa.