Cutar Sankarau ta Hallaka Mutane 20 a Jihar Jigawa
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce fiye da mutum 20 ne ake fargabar sun mutu sanadin cutar sanƙarau da ta ɓulla bana a jihar.
Jigawa, jiha ce da ke kan iyakar Najeriya da Jihar Damagaram, ta Jamhuriyar Nijar wadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da rahoto a makon jiya cewa mutum 18 sun mutu sanadin cutar ta sanƙarau da ta ɓarke a can.
Read Also:
Hukumomi a jihar Jigawa sun ce tuni suka gudanar da taron gaggawa da Hukumar Daƙile Cutuka ta Najeriya wadda ta yi alƙawarin aika riga-kafi ga mazauna yankunan kan iyaka.
Ga ƙarin bayanin da Dr. Salisu Mu’azu, Babban Sakataren a ma’aikatar lafiya ta Jigawa ya yi wa wakilinmu Zahraddeen Lawan
Ita dai cutar sankarau cuta ce wadda take da hadarin gaske da take shafar kwakwalwa da laka, kuma ta kasance babban kalubale ga duniya .
Kwayoyin baktiriya su ne suka fi haddasa ta.