Girgizar Kasa: An bukaci ‘Yan Najeriya su Taimaka wa Turkiyya da Syria

 

Ofishin jakadancin Turkiyya da ke Abuja da kuma kungiyar kare ‘yancin Musulmi ta Najeriya wato MURIC a takaice sun bukaci da a taimaka wa wadanda bala’in girgizar kasa ya afka wa a Turkiyya da Syria.

A sanarwar neman taimakon da ofishin jakadancin ya fitar jiya Lahadi a Abuja, ya bayyana irin kayayyakin da ake matukar bukata, wadanda suka hada da tufafi na sanyi da takalma da wanduna da safar hannu da safa da makamantansu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana kuma bukatar tantuna da gadaje da katifu da barguna da fulas da cocilan da jannareto da sauransu.

Harwayau, sanarwar ta bayyana irin bkayan abincin da ake bukata da suka kunshi abincin gwangwani da abincin jarirai na gwangwani da audugar kunzugu ta yara da ta mata da sauran kayayyakin bukata na tsaftar jiki da muhalli.

A ranar 6 ga watan Fabarairu ne girgizar kasa mai karfin gaske ta fada wa kasashen Turkiyya da Syria inda ta yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 30, tare da jikkata dubbai da lalata gidaje da kayayyaki.

A sanarwar an bayyana wuraren da za a kai kayan taimakon a Abuja lamba 46 Aminu Kano Crescent Wuse 2 sai da Lagos ARMADA International Limited 8 Solomon Agbontan Road (Aerodrome Road) Apapa.

Ita ma a sanarwar da ta fitar kungiyar kare muradun Musulmi ta Najeriya MURIC, kamar yadda Babban Darektanta Farfesa Ishaq Akintola, ya bukata, ta yi kira ga masu hali a Najeriya da su bayar da taimakon domin tallafa wa wadanda bala’in ya fada wa.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here