Muhammadu Sanusi II ya Bukaci Gwamnatin Najeriya da ta Saka Dokar Kayyade Yawan Iyali

 

Tubabben sarkin Kano, Sanusi II ya bukaci gwamnati da ta saka dokar kayyade yawan iyali.

Tsohon shugaban babban bankin ya ce hakan ne kawai zai kawo daidaituwar yawan ‘yan Najeriya.

Muhammadu Sanusi ya ce ba Musulunci bane haifar yaran da ba za a iya kula da su da kyau ba Tsohon sarkin Kano, Muhammad Sanusi II yayi kira ga gwamnati da ta saka tsauraran dokoki da za su daidaita hauhawar yawan jama’a a kasar nan.

Sanusi wanda yayi magana a ranar Laraba yayin wani taro a Legas, ya ce ya dace jama’a su dinga haifar yaran da za su iya kula da su, Daily Trust ta wallafa.

Sanusi ya kushe yadda ake haihuwa a kasar nan ba tare da karfin kula da yaran ba, wanda yace hakan ba daidai bane ko a addinin Musulunci.

Ya ce: “Yadda jama’a ke auren duk yawan matan da suke so ba tare da wata dokar da ta gindaya yawan yaran da za a haifa ba bai dace ba ko a Musulunci.

“Ban san dalili ba amma akwai doka a Musulunci da ta hana tara iyali ba tare da kayyade su ba. Babu wani tabbacin cewa za a iya kula dasu ba tare da an yi watsi da dawainiyarsu ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here