SANYA ANKLET, KO CHAINS A KAFA ;  A Mahangar Kimiyar Zamantakewar Dan Adam “Sociology”

 

Kimiyar Zamantakewar Dan Adam Wato “Sociology” ilimine dake nazari da duba kan halayya da dabi’ar Dan Adam, dakuma duba alaqarsa da sauran mutane cikin Al’umma baki daya Wato “Society”.

*MATSAYIN ANKLET KO CHAINS A FAHIMTAR SOCIOLOGY*

Kamar yadda komai na rayuwa ilimin Zamantakewar Dan Adam yayi magana akansa, haka yana kan magana akan sababbin Al’amari Wato *”new phenomena”*.

Sanya Anklets ko sarka (chains) a kafa, ilimin Zamantakewar bai barshi abaya ba. Domin fahimtar wannan Al’amari, Mutafi xuwa Daya (1) daga cikin Manyan Makarantun Sociology; Wato “Symbolic interactionism”

*MAKARANTAR SYMBOLIC INTERACTIONISM*

daya ce daga cikin Manyan Makarantun nazarin sociology (Sociological school of thought), ansamar da wannan Makaranta a 19th century, daga Manyan jigajiganta irinsu; C. H Cooley, G.H Mead, Erving Goffman dasauransu.

Fahimtar wannan Makaranta Shine; Ana iya fahimtar Dan Adam wajen isar da sako, batare da yafadi wani Abu ba (verbal expression), sedai ta hanyar nuni, motsi (gestures) ko wata alama (symbols) dayake isar da sako, wato ana kiransu “nonverbal means of communication”

Acikin wannan Makaranta (Symbolic interactionism), sun yarda cewa symbols yana isar da sako kamar yadda magana take isarwa, misali; duk sanda kaga mota da alamar L, yana nuna cewa dankoyo ne ma’ana Learner.

Haka; ajje alamar Triangle agaban mota idan anyi packed dinta yana nuna Motor ta lalace, ko Ana gyaranta. Misali na uku, ganin alamar upside U akan titi, yana nuna Ana iya yin U-turn awajen. Har ila yau, Ajje Alamar Abun xuba shara Wato “dustbin” agefen hanya; yana nufin zaka iya zubarda shara, babu laifi.

Bari mu dauki fahimtar Erving Goffman (1922-1982) a Wannan Makaranta ta Symbolic interactionism, Goffman yakawo wani nazarin sa mai suna “Tie Signs”.

*Erving Goffman’s Tie signs*

Babban Malami kuma professor a nazarin Halayya da Zamantakewar Dan Adam ta “Sociology”, yayi Nazari yasamar da Tie signs a shekarar 1959.

Tie signs wasu alamomi ne da suke dauke da ma’ana ko suke son isar da wani sako.

Misalin Tie signs ; Sanya zobe ga budurwar da akai mata baiko, Wato “Engagement” da kuma saka zoben a kowane yatsan hannun yana dauke da ma’anar sa. Dakuma Sanya Sarka a kafa, itama tana dauke da wannan ma’ana ta ta tadaban. Sbd haka Sanya Sarka a kafa yana daga cikin ire-iren “Tie signs”

*SANYA SARKA A KAFA KWALLIYA KO WATA ALAMA*

Kamar yadda ba bakon abu bane ;wato banbancin al’ada, abunda yake daidai a al’adar Bahaushe, ba dole bane yaxama daidai a al’adar inyamuri ko yoruba ba. Haka ba dole bane yayi daidai da al’adar wata Kasa ba…..

Adakacemu!

Domin cigaba daga inda aka tsaya.

Sameen Y Saeed (Dr.SYS) Dalibin Zamantakewar Dan Adam ne, kuma me Nazari da fashin Baki kan al’amuran Yau da kullum.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here