‘Yan Takarar Gwamna a Jahar Anambra Sun ƙulla Yarjejeniyar Zaman Lafiya

 

‘Yan takarar gwamna a Jihar Anambra da ke kudancin Najeriya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Awka, babban birnin jihar.

A ranar Asabar za a gudanar da zaɓen wanda yake fuskantar barazana daga ‘yan bindiga na ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) mai fafutikar kafa ƙasar Biafra.

An saka hannun ne ranar Alhamis a kan idon Shugaban Hukumar Zaɓe ta INEC Farfesa Mahmud Yakubu.

Kwamatin gina zaman lafiya na National Peace Committee ne ya shirya taron ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa Abdulsalami Abubakar.

Daga cikin ‘yan takarar akwai Ifeanyi Uba na

jam’iyyar YPP, Andy Uba na APC, Chukwuma Soludo na APGA, Valentine Ozigbo na PDP, Godwin Maduka na Accord Party (AP), Etiaba Chukwuogo na Action Alliance (AA).

Anambra kamar sauran jihohin kudu maso gabashin Najeriya, ta fuskanci tashin hankali iri-iri gabanin zaɓen, inda ‘yan bindiga suka tilasta wa ‘yan siyasa soke tarukan yaƙin neman zaɓe.

Ƙungiyar IPOB ta yi alwashin hana gudanar da zaɓen har sai an saki jagoranta Nnamdi Kanu wanda ke fuskantar shari’ar cin amanar ƙasa da haddasa tashin hankali.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here