Bukola Saraki ya Bayyana Aniyarsa ta Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2023
Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance, TheCable ta rawaito.
Saraki ya bayyana aniyarsa ne a wani taron karin kumallo da ‘yan jarida da wasu mukarrabansa a Abuja ranar Alhamis.
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce ya tsaya takara ne saboda akwai bukatar a magance matsalolin da suka addabi kasar nan na tsawon shekaru.
A kalamansa:
“Dukkanmu muna da dalilan da zai sa mu damu da makomar kasar nan. Amma wannan ba lokaci ba ne na mika wuya mu kuma yanke kauna.”
Maimakon cire rai da yanke kauna, Saraki ya shawarci ‘yan Najeriya da su samu kwarin gwiwa tare da jajircewa wajen tabbatar da kawo sauyi Najeriya.
Da yake tabo wani bangaren rayuwarsa, Saraki ya ce:
Read Also:
“Na yanke shawarar zama likita domin matukar sha’awar taimako da kuma yi wa wasu hidima.
“Kuma a 1999, na shiga gwamnati a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na kara fahimtar karin yin hidima ta hanyar gwamnati mara iyaka; da kuma yadda mulki na siyasa a hannun jagorori masu himma, cancanta da jajircewa zai iya magance matsaloli na hakika da kuma daukaka makomar kasa da al’ummarta.”
Saraki ya ce idan ya zama shugaban kasa zai kara habaka kudaden shiga daga bangaren da ba na mai ba.
A cewarsa:
“Matukar har yanzu a kasar nan akwai wadanda suke ganin za su iya karya dokokin Najeriya ba tare da wani hukunci ba; wadanda suke ganin laifin ba shi da wani sakamako, to ba a yi wani aiki ba.
“Kuma wannan shine dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa, saboda zan tabbatar da bin doka da oda tare da tabbatar da sakamako ga aikata laifuka.”
Karin bayani na nan tafe…