Tsoma Baki a Siyasa ba Aikin mu ba ne – Sarkin Bauchi ga Osinbajo

Sarkin Bauchi ya fitar da sanarwa ta musamman bayan ziyarar da Yemi Osinbajo ya kawo masa.

Hakan ya zama dole bayan an fara rade-radin Alhaji Rilwan Suleiman Adamu yana tare da Osinbajo.

Mai martaba ya bayyana ainihin abin da ya faru da Mataimakin shugaban kasa ya ziyarci fadarsa.

Bauchi – Mai martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwan Suleiman Adamu, ya karyata rahotannin cewa ya yi mubaya’a ga Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2023.

A wata takarda da majalisar Sarkin ta aikawa ‘yan jarida, wanda ya shigo hannun Legit.ng, Rilwan Suleiman Adamu ya ce ba ya cusa kansa a siyasa.

Wannan takarda ta fito ne a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu 2022, daga Babangida Hassan Jahun, wanda shi ne jami’in watsa labarai na masarautar Bauchi.

PM News ta ce masarautar ta yi karin-haske da cewa labaran da ke yawo a gari ba gaskiya ba ne, an kirkire su ne da nufin kawo rashin zaman lafiya a kasa.

Babangida Jahun ya ce abin da ya faru da Mataimakin shugaban kasar ya ziyarci fadar, shi ne Sarki ya fada masa tsoma baki a siyasa ba aikinsu ba ne.

A matasayinsa na Uba, Rilwan Suleiman Adamu ya ce nauyin da ke kansu shi ne bada shawara.

Me Sarki ya fadawa Osinbajo

“Ina so in yi maka maraba da zuwa jihar Bauchi. Na yi imani ka zo Bauchi domin harkokin siyasa ne, amma ka ga bukatar kawo mana ziyara duk da haka.”

“Wannan ya nuna irin kauna da kuma darajar da ka ba masarautar gargajiya.”

“Mun yarda cewa mulki yana hannun Ubangiji, shi ne yake bada shi ga wanda ya so. Haka zalika, mu ba ‘yan siyasa ba ne, na mu shi ne bada shawara.”

“Mu na addu’a ka samu nasara wajen yin duk abin da ya kawo ka Bauchi a yau. Duk abin da zai kawo hadin-kai da zaman lafiya shi mu ke goyon-baya.”

Ba a san sarakunan gargajiya da shiga harkar siyasa ba, don haka a al’ada ba su nuna fifiko a siyasa. An san su ne da bada shawarwari idan ana bukata.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here