Batanci ga Annabi Muhammad(S.A.W): Daliban Kwalejin Ilimin Shehu Shagari Sun Kashe Daliba

Sokoto- An kashe wata dalibar kwalejin ilmin Shehu Shagari dake jihar Sokoto bisa zargin batanci ga Annabi Muhammadu (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi)

21st CENTURY CHRONICLE ta ruwaito cewa an kashe dalibar mai suna Deborah bayan an bukaci ta janye kalamanta amma taki.

Rahoton ya kara da cewa wannan abu ya faru ne ranar Alhamis da safe.

Yanzu dai gwamnatin jihar Sokoto ta rufe makarantar, riwayar TVCNews.

Bidiyoyi a kafafen sada zumunta sun nuna yadda dalibai suka yiwa dalibar.

An tattaro cewa Deborah ta furta kalaman batancin ne a dakin kwanan dalibai sakamakon rashin jituwan da ya auku tsakaninta da wasu dalibai.

Daya daga cikin daliban da ta bukaci a sakaye sunanta tace:

“An bukaceta ta janye kalamanta amma ta ‘kiya, hakan ya fusata sauran dalibai Musulmai a kwalejin.”

Wata majiya ta bayyana cewa jami’an tsaron makarantar sun boyeta a ofishinsu amma fusatattun matasa suka fi karfinsu, suka kasheta, sannan suka kona gawarta.

Ance jami’an tsaro yanzu sun mamaye makarantar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here