Najeriya: Sarakunan Arewa Sun Nuna Damuwar su Akan Wasu Jahohi
Hankalin Sarakunan Arewa ya tashi a kan tabarbarewar ilimin yara mata a wasu jihohin yankin guda biyar.
Jihohin da abun ya shafa sune, Borno, Zamfara, Sokoto, Kebbi da kuma Gombe.
Sarakunan sun alakanta wannan kalubale da aka samu da rashin tsaro, tattalin arziki, jahilci da sauransu.
Wasu sarakunan Arewa sun nuna damuwa a kan tabarbarewar ilimin yara mata a wasu jihohin arewa guda biyar, jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sarakunan sun ce rashin tsaro, talauci, rashin ilimi da sauran kalubale, sune suke tabarbarar da ci gaban ilimin yara mata a jihohi irin Borno, Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi.
Sarkin Argungu kuma Shugaban gidauniyar Sultan na zaman lafiya da ci gaba, Samaila Mohammed Mera, ne ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Kaduna bayan taron kwanaki uku kan ajiye yara mata a makarantu.
Read Also:
Ya yi kira ga hukumomin da ya dace a kan su ci gaba da kara kaimi wajen wayar da kan jama’a a kan ilimin yara mata a yankin.
Ya ce taron ya tattauna “dalilin da yasa yaranmu mata basa makaranta, abunda ke hana su kammala karatunsu da kuma tsara dabaru kan hanyoyin tabbatar da ganin cewa sun sami ilimi domin amfanin al’ummansu.
“Muna da kalubale da yawa kan dalilin da yasa yaranmu mata ke barin makaranta. Wannan ya hada da jahilci, tattalin arziki, rashin tsaro.
Jihar Borno abun ya fi shafa saboda rashin tsaro, amma anan muna da Zamfara, Gombe, Sokoto da Kebbi, wanda a bisa ga alkaluma, sune mafi muni idan aka zo kan ilimin yara mata. Rangadinmu na gaba zai kasance kasar Ethiopia, inda karatun yara mata ke da karanci sosai.”
Fafutukar ajiye yara mata a makaranta a Afrika, Dr. Mairo Mandara, ta ce an shirya gangamin ne domin tabbatar da ganin cewa kowace yarinya ta kammala karatunta na makarantar sakandare.