Wata Kungiya ta Koka da Halin da Musulmai ke Fuskanta a Kudu

SEMON da Igbo Muslim Forum sun ce ana muzguna wa Musulmai a kasar Ibo.

Kungiyoyin sun ce Musulmai na fuskantar barazana na babu gaira, babu dalili.

Ana zargin CAN, Ohanaeze Ndigbo, da Gwamnoni da kauda fuskokinsu a gefe Kungiyoyin SEMON na Musulman Kudu maso gabashin Najeriya da Igbo Muslim Forum sun koka game da halin da ‘yanuwansu a addini su ke ciki.

SEMON da IMG sun yi tir da Ohanaeze Ndigbo da gwamnonin Kudu maso gabas da su ka yi shiru a lokacin da ake zargin ana yi wa Musulmai kisan gilla.

Wadannan kungiyoyi sun ce da gangan kungiyar IPOB ta ‘yan Biyafara su ka auka wa musulmai lokacin da ake zanga-zangar #EndSARS kwanakin baya.

Kungiyoyin sun fitar da wannan jawabi ne ta bakin shugaban kwamitin SEMON, Suleman Afikpo da Muhammad Amachi, kakakin Igbo Muslim Forum.

Suleman Afikpo da Muhammad Amachi sun ce ana kokarin danne Musulmai a yankin Kudu.

“Ko da zanga-zangar #EndSARS ta lafa, amma har yanzu Musulman Kudu maso gabashin kasar su na fuskantar ta’adi; Daga kisan gillar da aka yi wa Musulmai a Oyigbo, Onitsha, Aba da Orlu zuwa dagargaza masallatai da dukiyoyi da IPOB su ka yi.”

Kungiyoyin su ka ce an yi amfani da addini wajen ruguza masallatai biyu a garin Nsukka, Enugu.

Jawabin ya kuma ce: “Zama Musulmi a yankin gabashin Najeriya ya na da wahala. Harin da ake kai wa Musulmai a yankin, ya na kara karu wa ne kullum.”

A kullu yaumun, ana kai wa Musulmai hari na babu gaira babu dalili saboda kurum su na musulunci, sannan sun zargi CAN da gwamnoni da yin tsit.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here