Magu: Wasu Kungiyoyi Sun Bukaci Buhari ya Dakatar da Kwamitin Salami

HEDA da wasu Kungiyoyi su na so a dakatar da binciken Ibrahim Magu.

Kungiyoyin su na ganin kwamitin Ayo Salami ba zai iya yin adalci ba.

A ra’ayin wadannan kungiyoyi, binciken na iya kai wa ga abin kunya.

Kungiyoyin Human Environmental Development Agenda da wasunta sun nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da binciken Ibrahim Magu.

Wadannan kungiyoyi sun bukaci Muhammadu Buhari ta yi fatali da kwamitin Ayo Salami da aka kafa domin ya binciki zargin da ke wuyan Mista Ibrahim Magu.

Kungiyar wajen a takardar da ta aika wa shugaban kasar, ta ce zai yi wuya ayi wa Magu adalci.

The Cable da Premium Times sun rahoto cewa shugabannin HEDA, da kungiyoyin Global witness, Cornerhouse, da Re: Common sun sa hannu a wannan takarda.

Kungiyoyin nan su ka ce an dauki lokaci mai tsawo da sunan ana binciken tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC ba tare da an gano gaskiyar komai ba.

A dalilin wannan, kungiyoyin su ka nemi gwamnatin Buhari ta wargaza kwamitin Ayo Salami domin Najeriya ta guji yin abin kunya a gida da gaban Duniya.

A cewar kungiyoyin, ba su adawa da binciken hukumar EFCC, sai dai tsoronsu shi ne, tun farko an nuna kwamitin ba zai yi gaskiya a wajen wannan bincike ba.

Ya kamata Buhari ya san ana yi wa binciken da ake yi wa Magu kallon aikin banza ne kawai da yunkurin cin zarafin tsohon shugaban hukumar inji kungiyoyin.

Su ka ce kwanaki fiye da 120 kenan kwamitin da aka ba kwana 45 ya na aiki, amma babu abin da ya fito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here