Mafi Yawancin Wadanda Suke Karkasin Buhari Barayi ne – Ali Ndume

Buhari yana iyakar kokarinsa, mutanen da ke kasansa ne maanyan barayi, cewar Sanata Ali Ndume.

Sanatan kudancin Borno, Ali Ndume, yace ana cin amanar shugaban kasa Buhari ta karkashinsa.

Ndume ya fadi hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels.

Ali Ndume, sanata mai wakiltar kudancin Borno, ya ce da yawa daga cikin wadanda suke karkasin shugaban kasa Muhammadu Buhari barayi ne.

A ranar Lahadi, gidan talabijin din Channels sun yi hira da sanatan inda ya sanar da hakan, ya ce akwai mutanen da suke kokarin ganin bayan cigaba a mulkinsa.

Bayan an tambayeshi a kan yadda mulkin APC yake tafiya, cewa yayi gaskiya ba ya farinciki da tafiyar ta shekaru 5. Duk da suna yin iyakar kokarinsu, amma akwai gurabe da dama da ya kamata a cike.

A cewarsa, duk da kokarinsu, sai mutane sun zagesu, jaridar The Cable ta wallafa.

Ya ce shugaba Buhari sai dai ya bayar da umarni, amma ba zai iya zuwa yayi ayyuka da kansa ba, don haka mafi yawan matsalolin daga masu yin ayyukan ne.

Ya bayar da misalin yadda shugaba Buhari ya amince da biyan naira biliyan 500 don samarwa mutane ayyukan yi, musamman wadanda suka gama karatu kan fannin koyarwa.

Ya ce amma idan aka ji yawan mutanen da suka amfana, za a sha mamaki. Yawanci ba a dauka ba ma.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here