Daga Abdullahi Hashimu
Malan Lawal Maidoki, mutun ne mai amana kuma dattijo mai dattako ga dukkan al’amurran sa na yau da kullum.
Lawal Maidoki, ya kasance shi ne shugaba na farko da ya fara jagorantar Zakka da Wakafi a lokacin tsohuwar gwamnati ta Sanata Dr, Aliyu Magatakarda Wamakko.
Lokacin da Wamakko ya kirkiro da Zakka da Wakafi a jahar sakkwato, ya nemi da abashi mutun mai amana da jin tsoron Allah da kuma kamantawa a cikin harkokin yau da kullun don ya bashi jagorancin Zakka da Wakafi da ya kirkiro don taimkon al’umma jahar sakkwato musamman mabukata da marasa galihu.
Batare da bata lokaci ba aka kawo wa Wamakko, Malan Lawal maidoki, aka sheda masa cewa mutunne mai amana da kuma dattako da kishin addini da al’umma.
Wamakko ya nada Lawal maidoki a matsayin shugaban zakka da wakafi a jahar sakkwato, inda har gwamnati Wamakko ta cika wa’adin ta na mulki babu wani abu na rashin ya kamata da aka samu daga Maidoki kai hasalima sai Yabo da lambonin girma ya samu daga hukumomi daban-daban akan kyakyawan Jagoranci.
Ko jagoranci Maidoki na Zakka da Wakafi ya biya bukatar gwamnatin Wamakko?
Read Also:
Hakika kwalliya ta biya kuddin sabulu, a jagorancin da Lawal Maidoki yayi a lokacin gwambatin Wamakko, sabo da dukkan gundumomin jahar sakkwato babu inda alhairin jagorancin maidoki bai kai ba.
Al’umma sun shiga cikin jindadi da walwala ta hanayar samun tallafi na kuddi da abinci da magani da kuma taimako da karfafa wasu ta hanayar basu jari don yin sana’a da kuma Aurar da mata da tallafawa gajiyayu da marasa galihu da uwa uba Marayu.
Zuwan Gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal ta cigaba da aiki Lawal Maidoki, inda ta mayar da zakka da wakafi zuwa hukuma Wadda zataci gashin kanta Hukumar Zakka DA Wakafi. kuma ta bar Malan Lawal Maidoki a matsayin shugaban wannan hukuma mai zaman kanta sabo da rikon amana da iya jagoranci.
Kasan cewar kowace rayuwa ta dan Adam tana da nata guri da take so ta cimma a duk Inda ta samu kanta a cikin rayuwar yau da kullun.
Shin ko Mine ne Gurin Malan Lawal Maidoki?
Wane dalili ne yasa mai Alfarma Sarkin Musulmi ya nada Malan Lawal maidoki matsayin Sadaukin Sakkwato?
Masu karatu suna son su san minene ma’anar Kalmar Sadauki?
Domin jin amsoshin wadan nan zafafan tambayoyi sai ku kasance damu zuwa karshen mako, Inda zakuji daga bakin Lawal Maidoki.
Abdullahi Hashimu
2, June, 2019.
The post Sarautar Sadaukin Sakkwato, ta dace da Malan Lawal Maidoki appeared first on Daily Nigerian Hausa.