Sarkin Katsina ya Naɗa Justice Adamu Bello a Matsayin Sabon Hakimin Kanƙara
Sarkin Katsina, Mai Martaba Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa sabon hakimin Kanƙara.
Wannan ya faru ne bayan tsige wancan da majalisar sarkin tayi inda ta kama shi da hannu dumu-dumu wajen taimaka wa yan bindiga.
Sarkin ya naɗa Justice Adamu Bello a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kanƙara Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, ya naɗa sabon sarkin Pauwan Katsina, Hakimin Kanƙara.
Read Also:
Wannan na zuwa ne bayan sarkin ya tsige tsohon hakimin, Alhaji Yusuf Lawal, bayan gano cewa yana taimaka wa yan bindigan da suka addabi jahar.
Sarkin ya naɗa Justice Adamu Bello a matsayin wanda zai maye gurbin Sarkin Pauwan Katsina Hakimin Kanƙara.
Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da Katsina Daily Post ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta Facebook. Rahoton naɗin ya bayyana cewa Sarkin Labaran Majalisar sarkin Katsina, shine ya tabbatar da wannan sabon naɗin da sarki yayi.
Legit.ng hausa ta kawo muku rahoto cewa bayan gano tsohon hakimin Kankara na da hannu a hare-haren yan Bindiga, majalisar sarkin ta yanke shawarar tumɓuke shi daga muƙaminsa.