Sassa 20 da Ake sa Ran su Zama Sababbin Jahohi a Najeriya
Majalisar dattawa ta karbi rahoton koke daga yankuna daban-daban na Najeriya kan gyara kudin tsarin mulki.
A halin yanzu, an ware wasu sassa 20 da ake sa ran su zama sabbin jahohi a Najeriya nan gaba.
Legit ta kawo muku jerin jahohin da kuma in da za a rabe su su zama jahohi masu zaman kansu.
Kwamitin majalisar dattawa kan sake duba kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da shawarar a kirkiro sabbin jahohi 20.
Kwamitin ya cimma wannan matsaya ne bayan ya duba abubuwa daban-daban da suka hada da ikon gwamnatin farar hula na kirkiro jahohi.
Majiyoyi sun shaida wa jaridar The Nation cewa ana iya gudanar da zaben raba gardama a kasa da jahohi 20.
Read Also:
Kwamitin ya ba da shawarar ba da matsayin jiha ga FCT. An ce jerin bukatun kafa sabbin jahohi sun yi tsawo sosai.
Su ne kamar haka:
1) Jahar ITAI daga Akwa Ibom
2) Jahar Katagum daga Bauchi
3) Jahar Okura daga Kogi ta Gabas
4) Jahar Adada daga Enugu
5) Jahar Gurara daga Kaduna ta Kudu
6) Jahar Ijebu daga Ogun
7) Jahar Ibadan daga Oyo
8) Jahar Tiga daga Kano
9) Jahar Ghari daga Kano
10) Jahar Amana daga Adamawa
11) Jahar Gongola daga Adamawa
12) Jahar Mambilla daga Taraba
13) Jahar Savannah daga Borno
14) Jahar Okun daga Kogi
15) Jahar Etiti daga shiyyar kudu maso gabas
16) Jahar Orashi daga Imo da Anambra Njaba daga jahar Imo ta yanzu ko rabewar
17) jahar Aba daga Abia
18) Jahar Anioma daga Delta
19)Jahohin Torogbene da Oil River, daga jahohin Bayelsa, Delta da Ribas
20)Jahar Bayajida daga sassan Katsina, Jigawa da Zamfara