Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Obasanjo ya Kai Ziyara Jamhuriyar Benin a Boye

 

An gano yadda tsohon shugaban kasar Najeriya ya kai ziyara a boye zuwa jamhuriyar Benin a makon farko na watan Augustan 2021.

Labarai sun bayyana akan yadda tsohon shugaban kasar ya biya Zanzibar, wani tsibiri dake Tanzania a ranar 1 ga watan Aungusta.

kafin ya wuce Benin Ya je jamhuriyar Benin din ne don yin ta’aziyya ga Nicephore Saglo bisa mutuwar matarsa wata majiyar kuma tace akan lamarin Igboho yaje.

Cotonou – Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara jamhuriyar Benin a makon farko na Augustan 2021 kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Manyan majiyoyi sun sanar da theCable cewa sai da tsohon shugaban kasar ya biya ta tsibirin Zanzibar dake Tanzania a ranar 1 ga watan Augusta kafin ya wuce Benin din.

Obasanjo yaje ziyarar ta’aziyya

Ya kai ziyarar ne don yin ta’aziyya ga Nicephore Soglo wanda bai dade da rasa matarsa Roseline Soglo ba.

Roseline ta rasu ne a ranar 25 ga watan Yuli tana da shekaru 87 a Cotonou.

Soglo tsohon Shugaban kasar Jamhuriyar Benin ne daga 1991 zuwa 1996.

TheCable ta fahimci tsohon shugaban kasa Obasanjo da Sangolo sun rike abotarsu na tsawon shekaru da danko mai karfi.

Soglo yana daya daga cikin shugabannin Afirka wanda yasa baki a lokacin Abacha aka kama Obasanjo kuma aka daure shi a 1995.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya kai ziyara Zanzibar a ranar 1 ga watan Augusta don ya boye tafiyarsa zuwa jamhuriyar Benin, kamar yadda daya daga cikin majiyoyin ya shaida.

Yaje yi wa tsohon shugaban kasa Sogholo ta’aziyya ne bisa rasa matarsa da yayi a ‘yan kwanakin nan.

Boyayyar tafiya Obasanjo yayi

Wata majiyar kuma ta ce Obasanjo ya boye tafiyar ne: Ya hadu da Patrice Talon.

Dalilin haduwarsu shine don ya samu kyakkyawan masauki ga Sunday Igboho. Yana bukatar Benin ta samar wa da Igboho masauki mai kyau kuma kada ta bari ya dawo Najeriya.

Tsohon shugaban kasar ya bukaci wasu daga cikin shugabannin kudu maso yamma da su sanya baki akan lamarin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here