Hukumomin Saudiyya sun kai Samame Kasuwannin ƙasar Don Lura da Farashin Kayayyaki

 

Ma’aikatar kasuwanci ta ƙasar Saudiyya ta ce ta tura tawagar masu sanya ido domin duba kasuwanni a biranen Makka da Madina don lura da farashin kayayyaki a cikin watan Ramadan.

Tawagar masu sanya idon waɗanda ke aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sauran hukumomi, an ƙaddamar da ita ne da nufin duba ko ‘yan kasuwa na biyayya ga dokokin kare haƙƙin mai saye ko akasin haka.

Haka kuma hukumar ta ce aikin wani ɓangare ne na aikin da ma’aikatar ke gudanarwa domin tabbatar da wadatuwar kayyakin masarufi da za su wadaci ‘yan ƙasar, tare da samun hanyar da za a wadata kasuwanni da kayayyaki.

Tawagar masu sanya idon na tsaurara bincike a shagunan da ke kan titunan biranen Makka da Madina, musamman a wannan lokaci da ake samun yawaitar masu Umrah a ƙasar.

Haka kuma suna duba gidajen mai da shagunan sayar da kayyayakin gyaran ababen hawa, domin tabbatar da ‘yan kasuwa na bin umarnin ƙayyade farashi da ma’aikatar ta sanya.

Tun kafin fara azumin watan Ramadan ma’aikatar ta ɗauki matakai domin samar da wadatattaun kayayyakin buƙatun azumin a kasuwannin ƙasar, da kuma tabbatar da ingancinsu.

Tare kuma da duba kayayyakin da kwanan watan lalacewarsu ya cika domin ɗaukar matakan shari’a kan ‘yan kasuwar da suka ƙi fitar da su daga shagunansu.

Ma’aikatar ta kuma buƙaci masu sayen kayyakin da su kai rahoton duk wani ƙorafi da suke da shi kan wani ɗan kasuwa da suka zarga da aikata ha’inci a kasuwancinsa, ta hanyar bayar da lambobin wayar da za a tuntuɓi ma’aikatar

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here