Saudiyya za ta Karɓi Baƙunci Mahajjata Miliyan Biyu a Bana
Saudiyya na shirin karɓar baƙuncin mahajjata miliyan biyu daga faɗin duniya a wannan shekarar ta 1444, kamar yadda Ministan Hajji da Umrah Dr Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana.
Dr. Al-Rabiah ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara zuwa Algeria a hukumance, inda ya bayyana cewa za a bai wa Algeria kujera 41,3000 ta mahajjatan bana.
Read Also:
Saudiyya ta ce za ta yi farin cikin karɓar mahajjatan bana kan adadin da aka saba a baya gabanin zuwan annobar corona.Ministan ya bayyana yadda ma’aikatarsa da sauran hukumomin da suke da hannu a aikin hajji da umra suka shirya domin kula da tsarin lafiya da sauran aikace-aikace ga mahajjata.A watan Dismbar da ya gabata ne, Saudiya ta dawo wa da Najeriya adadin kujerun da ta saba ba ta sama da 95, 000, na mutanen da za su je aikin.