Gwamnatin Katsina ta Ayyana Hutun Kwana 2 Saboda Ziyarar Shugaba Buhari

 

Gwamnatin Jihar Katsina da ke arewacin Najeriya ta ayyana yau da gobe a matsayin ranakun da babu aiki, domin bai wa ma’aikata damar tarbar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari yayin ziyarar da zai yi ta kwana biyu a jihar.

Cikin wata sanarwa da babban sakataren ma’aikatar yaɗa labarai da al’adu Sani Bala Kabomo ya fitar.

Ya ce hutun da aka bayar zai taimakawa ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi da na sauran hukumomi damar yi wa Shugaba Buhari barka da zuwa.

Ya ƙara da cewa hutun ba zai shafi ayyukan tarayya da na bankuna ko kuma manyan ayyuka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here