Sokoto: Jama’a Sun Koka Kan Yadda ‘Yan Kasuwa Suka Dai na Karbar Tsofaffin Kudi

 

 

Mazauna jihar Sakkwato sun shiga cikin rudani bayan masu saide-saide sun murje ido sun ki amsar tsofaffin kudi.

Duk da hakan, bankuna na cigaba da bada tsoffin kudi ga kwastomomi da ikirarin basu da sabbi, wanda hakan ya tada hankulan mutane ganin yadda kudadensu ke dab da zama takardun tsire.

An gano yadda masu shaguna, ‘yan acaba da sauran masu kasuwanci suka ki amsar tsofaffin kudin, yayin da wasu suka garkame shagunansu gudun kada a kawo musu kudin da zasu daina aiki a hannunsu.

Sokoto – An samu matsanancin rudani a jihar Sakkwato yayin ‘yan jihar da dama sukaki amsar tsohon kudi daga kwastomomi.

Wakilin Punch wanda ya ga yadda lamarin ya auku a fadin jihar ranar Litinin ya tattaro yadda ‘yan kasuwa da dama a fadin jihar suka fara kin amsar tsofaffin kudi.

Haka zalika, an tattaro yadda ‘yan acaba suka ki amsar wannan kudin daga fasinjojinsu.

Yayin zantawa da wakilin Punch, wani mazaunin jihar, Atiku Abdulrafiu, yayi kira ga Babban Bankin Tarayya Najeriya da Gwamnatin Tarayya da su samo mafita don kara wa’adin karbar tsoffin kudi kafin sabbin su yi yawa.

Ya bayyana yadda a yau, bankuna da dama a jihar suke ba kwastomomi wadannan tsoffin kudin.

“Na je banki yau don cire kudi, mun cire N580,000 amma ka san wani abu? Duk kudin da aka bamu tsoffi ne. Mun bukaci sabbin kudi, amma ga mamakinmu, suka ce basu da sabon kudi.

“Yanzu, taya za ka ji idan ‘yan masu saide-saide suka ki karabar wadannan kudin a wannan jihar.”

Har ila yau yayin zantawa da wani mai saide-saide a tsohuwar kasuwar Sakkwato, Alhaji Isa Sa’a, ya ce ya yanke shawarar kin bude shagonsa har zuwa karshen watan nan don tsoron amsar tsoffin kudi.

A cewarsa:

“Na shaidawa kwastomomina kada su yi yunkurin zuwa shagona sai wani watan saboda ba zan fito kasuwa ba.

“Ba na son amsar kudin da zai daina amfani a gidana.”

Sai dai, yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta duba halin da ‘yan Najeriya ke ciki ta kara wa’adin amsar tsoffin kudi don sabbi su yadu.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here