An Fara Sayar da Buhun Shinkafa a Kan N40,000
Jihar Ogun – Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin sayar da shinkafa a farashi mai rahusa a jihohin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa a ranar Alhamis ne aka ƙaddamar da shirin a jihar Ogun kafin fara shi a sauran jihohin Najeriya.
Vanguard ta wallafa cewa daraktan ma’aikatar noma da samar da abinci ne ya wakilci ministan noma, Sanata Abubakar Kyari.
An fara sayar da buhun shinkafa a N40,000
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin sayar da buhun shinkafa a kan N40,000 a Abeokuta na jihar Ogun.
Read Also:
Ma’aikatar noma ta bayyana cewa za a yi adalci wajen tabbatar da cewa waɗanda suka cancanta ne suke sayen shinkafar.
Sharadin sayen buhun shinkafar N40,000
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk wanda zai saye shinkafar dole ya nuna lambar shaidar zama ɗan kasa ta NIN.
Haka zalika masu sayen shinkafar za su zo da katin banki na ATM da za a zare kudin saboda ba kudi a hannu za a yi cikin ba.
Dalilin fara sayar da shinkafa a Ogun
Ma’aikatar noma ta bayyana cewa fara da jihar Ogun ne kasancewar yadda gwamna Dapo Abiodun ya ke nuna salon shugabanci mai kyau.
Rahoton Channels Television ya nuna gwamna Dapo Abiodun ya mika godiya ga shugaba Bola Tinubu kan kawo shirin sayar da shinkafar.