Kungiyar SERAP ta Bukaci da a Dakatar da Katse Hanyoyin Sadarwa na Jahar Zamfara da Katsina
Kungiyar SERAP ta bukaci shugaban ƙasa Buhari ya gaggauta dakatar da matakin datse sabis a Zamfara da Katsina.
A cewar kungiyar wannan matakin ya kara wa al’ummar yankin matsin rayuwa banda wanda suke ciki a baya.
Hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa su datse hanyoyin sadarwa a Zamfara da wasu kananan hukumomi a Katsina
Abuja – Ƙungiyar dake fafutukar ganin anyi adalci a sha’anin mulki, SERAP, ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin tarayya na datse sabis ɗin sadarwa a Zamfara da Katsina, kamar yadda dailytrust ta rawaito.
Wannan dai ya biyo bayan halin tasku da al’umma suka shiga a jahar Zamfara da wasu sassa na Katsina kan datse hanyoyin sadarwa da FG ta yi.
SERAP ta yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci ma’ikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) su yi saurin dawo da sabis a dukkan yankunan da lamarin ya shafa.
Read Also:
Kungiyar ra roki shugaba Buhari kan ya gaggauta umartar ministan sadarwa, Dakta Isa Pantami, ya maida harkokin sadarwa kamar da a Zamfara da Kananan hukumomin 13 da abun ya shafa a Katsina.
Meyasa aka katse sadarwa?
A kwanakin baya hukumar NCC ta umarci kamfanonin sadarwa da su dakatar da ayyukansu a faɗin jahar Zamfara, kamar yadda Tribune ta rawaito.
Legit.ng hausa ta rahoto muku cewa hukumomi sun sake umartar kamfanonin su ɗauke sabis ɗin sadarwa a kananan hukumomi 13 daga cikin 34 na jahar Katsina.
Sakon SERAP ga Shugaba Buhari
Sai dai wannan matakin baiwa kungiyar SERAP daɗi ba, inda ta aike da wata wasika ga shugaba Buhari, mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar, Kolawole Oluwadare.
Wani sashin wasikar yace:
“Datse sabis da sauran harkokin sadarwa a Jahohin Zamfara da Katsina, ba tare da wata kwakkwarar hujja ba ya saba wa doka da hankalin duk wani mai tunani.”
“Katse hanyoyin na sadarwa wani mataki ne na hukunta ’yan Najeriya da ke zaune a waɗannan yankuna duk kuwa da yanayin matsi da suke ciki tun asali.”