Dangin Igboho Sun Gargadi Sheikh Gumi Kan Zuwa Yankinsu

 

Shugabanni a yankin Yarbawa sun gargadi Sheikh Gumi kan zuwa yankin su Sunday Igboho.

Wannan na zuwa ne bayan da malamin ya ziyarci garinsu Sunday Igboho a makon da ya gabata.

Ciki har da mahaifiyar Igboho, an yi addu’o’in wanke sharrin da malamin (Gumi) ya zo dashi yankin.

Igboho, jahar Oyo – Magoya bayan dan awaren yarbawa Sunday Igboho, mahaifiyarsa da danginsa sun gargadi malamin addinin musulunci dan Arewa, Sheikh Ahmad Gumi da ya nesanta kansa daga kasar Yarbawa.

Sun bayyana ziyarar da Gumi ya kai garinsu Igboho a matsayin abin ”tuhuma” kuma ”rashin hankali ‘.

Igboho, dan shekaru 48 a halin yanzu yana garkame a hannun jami’an jamhuriyar Benin bisa wasu laifuka ciki har da kutse cikin kasa ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun bazu a kafafen sada zumunta inda aka ga Sheikh Gumi tare da tsohon babban jami’in hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS), Usman Yusuf a kusa allon makarantae ‘Muslim Grammar School, Modeke, Igboho’ a ranar 7 ga watan Satumba.

Da yake magana yayin ziyarar, malamin ya ce da abin da ya gani, babu bukatar wata kungiya ta nemi ballewa daga Najeriya.

A wani bidiyon bidiyo da The Nation tace ta samu a karshen mako, Sheikh Abdul Raheem Aduanigba, Babban Limamin Yarbawa a Ilorin, ya jagoranci wasu shugabanni zuwa garin Igboho tare da mahaifiyar Igboho.

Sun ziyarci wurin da Gumi ya yi wancan bidiyon yayin ziyararsa a garin sannan kuma sun yi addu’o’i don rushe munanan dalilai da suka kawo Gumi garin.

Ya ce:

“Ba mu san lokacin da Gumi ya zo nan ba, Igboho bai damu da dukiyarsa ba, ya kan kashe kudi da yawa. Ya kan kula da kowa har da Musulmai.

“Muna addu’ar nasara don a saki Igboho. Allah zai daow da Igboho gida lafiya ya sadu da mahaifiyarsa. Allah ya kiyaye Igboho ya ba shi tsawon rai. Babu zaman lafiya a Najeriya. Dole ne mu yi taka tsan-tsan a Najeriya.”

Daya daga cikin abokan Igboho, Alhaji Yusuf Saheed wanda aka fi sani da Ajikobi 1 ya ce:

“Shi (Gumi) kawai ya zo nan cikin rashin sani ne, kuma ya yi amfani da kusan mintuna 3. Igboho mutum ne mai karfin ikon gaske, duk da tsoratarwar da gwamnati ke yi masa, har yanzu yana nan daram.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here