SERAP ta Soki Karin Kudin Fetur

 

Abuja – Kungiyar kare hakkin jama’a da tattalin arzikin kasa (SERAP) ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya umurci kamfanin NNPCL ya gaggauta janye karin kudin fetur.

A wata wasika mai kwanan wata 7 ga Satumba 2024 daga mataimakin daraktanta, Kolawole Oluwadare, SERAP ta yi ikirarin cewa karin kudin man ya sabawa ka’ida

A wasikar da ta wallafa a shafinta na intanet, SERAP ta ce karin kudin man ya take wani bangare na kundin tsarin mulki da kuma hakkokin bi Adama na kasa da kasa.

SERAP ta soki karin kudin fetur

SERAP ta bukaci shugaban kasar da ya yi amfani da karfin ikonsa domin”ya umarci kamfanin NNPCL ya janye wannan karin man da ya yi wanda ya saba doka da tsari.”

“An dade ana takewa ‘yan Najeriya ‘yancinsu da kuma hana su sanin dalilin da ya sa suke ci gaba da biyan kudaden almundahana a bangaren mai.

“Ƙarin farashin man fetur ya kara jefa ‘yan ƙasa cikin mawuyacin hali wadanda dama can suna fama da talauci ba tare da iya biyan buƙatun su na rayuwa ba.

Kara fashin bai zama dole ba, domin ya samo asali ne daga gazawar gwamnatocin da suka shude wajen magance zarge-zargen cin hanci da rashawa a bangaren mai.”

– A cewar SERAP.

SERAP na so a binciki NNPCL SERAP ta kuma bukaci Tinubu da ya umarci ministan shari’a, Lateef Fagbemi da hukumomin yaki da rashawa da su binciki zargin cin hanci da rashawa a cikin kamfanin NNPC.

“Cin hanci da rashawa a bangaren mai tare da rashin gaskiya da rikon amana wajen amfani da kudaden gwamnati a ayyukan NNPC, ya haifar da kara kudin mai ba bisa ka’ida ba.

“Tuhuma da bincikar kamfanin mai na NNPC kan zargin laifuffukan cin hanci da rashawa a bangaren mai zai zama biyan bukatar ‘yan kasar.

Mun damu kwarai da yadda tattalin arzikin Najeriya ke kara tabarbarewa, wanda karin farashin man fetur zai kara jefa mutane cikin talauci.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here