Gwamnan Oyo Yayi Alkawarin Bawa Sarkin Ogbomoso N90m don Gyara Fadarsa
Sarkin Ogbomoso ya ki karbar naira miliyan 10 daga cikin naira miliyan 100 da gwamna Seyi Makinde ya yi alkawarin bashi, An yi alkawarin bada naira miliyan 100 ne don yin gyare-gyare a fadar sarkin sakamakon barnar da bata gari suka yi yayin zanga zangar EndSARS – Sarkin ya bayyana cewa ainihin mazauna garin maza da mata sun yi alkawarin za su yi wa fadar garambawul.
Read Also:
Sarkin al’ummar Kasar Ogbomoso, Oba Oladunni Oyewuni III ya ki karbar tallafin Naira miliyan 100 daga gwamnan Jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde. Gwamnan yace an ware kudin ne don amfani dasu wajen gyara ɓarnar da akayi wa fadar Ogbomoso mai daɗaɗɗen tarihi, wanda yan ta’adda da yan tawaye da suka fake da zanga zangar #ENDSARS suka aikata. Sai dai, a wata takarda mai dauke da kwanan wata 19 ga Oktoba 2020, da aka aikewa gwamnan, ta nuna cewa kudaden gyaran fadar da aka lalata zasu fito daga hannun al’ummar yanki Ogbomoso tare da miliyan 10 da gwamnan ya riga ya bayar.
Sarkin ya yi wa gwamnan godiya amma ya ce babu bukatar ware makuden kudin domin yi masa gyare-gyare a fadarsa. A cewar My Woven Words, sarkin na Ogbomoso ya ce naira miliyan 10 da aka bashi nan take bayan harin ya wadatar ba sai an ciko masa naira miliyan 90 din ba. Sarkin ya ce wasu mazauna garin sun yi alkawarin yin gyare-gyaren.
Sai dai sarkin ya bukaci Seyi Makinde ya samar da ayyukan yi ga dimbin matasa da ke zaman banza a jihar.