2023: Mutane 5 Daga Jam’iyar PDP Sun Fitar da Gwaninsu Wanda Zai Gaji Buhari

Jam’iyyar PDP reshen Ebonyi ta yi barazanar sanya kafar wando daya da shugabanninta na kasa idan ba a mika tikitin zaben shugaban kasa na 2023 zuwa yankin kudu maso gabas ba

Reshen ta bayyana cewa yankin na da kwararrun mutane da za su iya karbar ragamar shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari idan mulkinsa ya kare – Jam’iyyar ta ambaci tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, Peter Obi, masaniyar tattalin arziki, Ngozi Okonjo Iweala a matsayin mutane da suka gogu Yayinda ake ci gaba da tattaunawa kan 2023, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Ebonyi ta bukaci jam’iyyar da ta mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu maso gabas. Shugaban PDP a jihar, Onyekachi Nwebonyi, ya yi wannan rokon a yayinda yake jawabi ga manema labarai a Abakaliki a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

Nwebonyi ya yi gargadin cewa za a kwashi yan kallo Idan shugabancin jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Uche Secondus, bata bai wa yankin kudu maso gabas tikitin ba. Ya bayyana cewa idan shugaban jam’iyyar na kasa ya ki aiwatar da bukatar, hakan zai haifar da rashin jin dadi kuma yana iya dakushe damar PDP na lashe zaben 2023.

Shugaban na PDP a Ebonyi ya jadadda cewa mika tikitin shugaban kasa na jam’iyyar zai tabbatar da adalci da daidaito, inda ya kara da cewa za su marawa Secondus baya domin ya zarce.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here