Sharudda Dage Dakatar da Twitter: Gwamnatin Tarayya ta Musanta Batun

 

Gwamnatin tarayya ta musanta rahoton dake yawo na cewa ta bada sharadi kafin ta dage dakatar da Twitter da tayi a kasar nan.

Ferdinand Nwonye, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, ya sanar da hakan a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni a Abuja.

Nwonye ya kara bayanin cewa ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya tattauna da wasu wakilai, ba a fahimci bayaninsa bane.

Ma’aikatar harkokin waje a ranar Litinin, 7 ga watan Yuni, ta ce gwamnatin tarayya bata zayyana wasu sharudda ba da za ta saka a dage dakatar da Twitter da aka yi a kasar nan.

Legit.ng ta ruwaito cewa hakan yana kunshe a wata takarda da mai magana da yawun ma’aikatar, Ferdinand Nwonye, ya fitar.

Takardar mai taken, “Karin bayani kan tsokacin mai girma ministan harkokin waje a wurin taro da wakilai.”

Nwonye yace ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya gana da tawagar Amurka, kungiyar gamayyar Turai, Jamhuriyar Ireland da Canada a ranar Litinin a Abuja a kan tsokacin da yasa gwamnati ta dakatar da Twitter a Najeriya.

Ya kara da cewa abokai biyar sun saka hannu kan wata takarda a ranar Asabar, 5 ga watan Yuni inda ta kushe dakatar da Twitter a Najeriya tare da kwatanta shi da take hakkin dan Adam.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here