Zan Karfafa Cin Naman Alade a Madadin Naman Shanu a Jahata – Gwamna Rotimi Akeredolu
Gwamnan jahar Ondo ya bayyana aniyarsa ta karfafa maciya naman alade a duk fadin jahar.
Ya ce gwamnatinsa a shirye take don maye gurbin naman shanu da naman alade a fadin jahar.
A cewarsa, jahar na asarar kudaden da ya kamata a jahar za a kashesu ga wasu jahohin daban.
Gwamnan jahar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya ce gwamnatinsa za ta karfafa cin naman alade a madadin naman shanu don tattala miliyoyin nairorin da jahar ke asara ga sauran jahohin da ke samar da naman shanu da sauran nau’ikan nama, Daily Trust ta ruwaito.
Read Also:
Akeredolu ya fadi haka ne a ranar Litinin yayin kaddamar da wani babban mayankar alade ta Dutchman Piggery da kayan tallafi a Ilutoro da ke karamar hukumar Akure ta Arewa a jahar a matsayin wani bangare na ayyukan cikarsa kwanaki 100 a ofis.
A cewar gwamnan, kudin da ake kashewa ga wasu jihohin da ke samar da shanu da sauran nau’ikan nama zasu kasance a jihar don kara tattalin arzikin jahar.
Ya kuma ce baya ga ayyukan ta da zai samar wa matasa, za a karfafawa masu cin naman alade, naman alade kuma zai zama madadin naman shanu a jahar.
“Bugu da kari, za a kuma karfafa yankunan mu na karkara don ci gaba.
“Abin mamaki ne cewa miliyoyin Nairori suna barin wannan Jaha duk mako saboda cin naman shanu.
A baya an samu tangarda tsakanin gwamnatin jahar ta Ondo da makiyaya dake zaune a yankunan jahar, lamarin da ya kai ga ba da umarnin fatattakar makiyaya a fadin Ondo, Vanguard ta ruwaito.