Dakatar da Twitter: Gwamnonin APC Biyu Sun Saba Umarnin Shugaba Buhari

 

Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnonin APC biyu sun bijirewa umarnin gwamnati na dakatar da Twitter.

An ga rubutun gwamnonin biyu biyo bayan dakatar da ayyukan Twitter a fadin kasar ta Najeriya.

Sai dai, an bayyana wasu dalilai da suka ja wadannan gwamnoni suka yi amfani da shafin na Twitter.

Biyo bayan umarnin gwamnatin tarayya na dakatar ayyukan Twitter a Najeriya, an samu wasu gwamnonin Najeriya da suka yi kunnen kashi suka yi rubutu a shafin na Twitter.

Gwamnonin jahohin Kaduna da Ondo, Nasir El-Rufai da Rotimi Akeredolu, suka bijirewa wannan umarni na gwamnati, Premium Times ta ruwaito.

Dukkanin gwamnonin, wadanda suke mambobin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi rubutun a Twitter, ba tare da tsoron barazanar Babban Lauyan Tarayya da Ministan Shari’a, Abubakar Malami na hukunta masu yin Twitter ba.

El-Rufai, daidai karfe 9:37 na dare a ranar Lahadi, ya ba da labarin ra’ayi mai taken “Based Nigeria: African country teaches US lesson in how to handle Big Tech tyranny”.

Labarin wanda Nebojsa Malic, wani dan jarida Ba-Amurke ne ya wallafa, ya ba da dalilin dakatar da shafin na Twitter, inda ya ja hankalin Amurka don daukar darasi daga matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka.

Gwamna Akeredolu, a daya bangaren kuwa, ya fitar da sanarwa dangane da wani harin wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama a yankin Igangan da ke jahar Oyo a ranar Lahadi.

Ya yi magana ne kan kashe-kashen a matsayinsa na Shugaban kungiyar Gwamnonin Kudu maso Yamma.

“Mu, a namu bangaren, mun yanke shawarar kare mutanenmu, da dukiyoyinsu, da duk wata hanyar da ta dace ciki da na waje.

A kan wannan, ba za a yi sulhu ba,” sanarwar ta karanta. Majiyoyin gwamnati sun shaida cewa Gwamna El-Rufai ya kasance a wajen kasar sama da mako guda. Duk da cewa majiyar ba ta bayyana inda yake ba, amma ta ce “ba a dakatar da ayyukan Twitter a kasar ba.”

Lokacin da aka tuntube shi, kakakin Gwamna Akeredolu, Olabode Richard, ya ce ‘yan Najeriya na iya hawa kafar Twitter a ranar Lahadi, ya kara da cewa shugaban na sa bai yi amfani da Virtual Private Network (VPN) ko wasu hanyoyin da ‘yan Najeriya ke bi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here