Shugaban ƙasa Shehu Aliyu Usman Shagari ya bar duniya da shekara 93. Ya yi rayuwa mai tsawo mai albarka. Ya bar zuri’a mai yawa mai albarkar da kowa ƙasar nan da ma wajenta ya na son alaƙanta kan shi da ita. Daga ƙarshe ya rabu da duniya lafiya kuma cikin aminci wanda ya sa al’umma ta ji zafin rabuwa da shi.

Shehu Shagari bai yi zurfi a karatun zamani ba, amma ya bar ilmi da hikimar da jami’o’i za su kamfata su sha kuma su shayar da wasu har su bar saura. Ta rayuwar Shehu Shagari ne na ƙara tabbatar da cewa tarin karatu daban, ilmi daban.

A raye ko a mace, sunan “Shagari” ya taimaki mutane da yawa. Na san mutanen da sunan Shagari a matsayin gari, da ke maƙale da sunansu, ya sa sun samu girmamawa a kudanci da ma wajen ƙasar nan. Wani ya bani labarin yadda ya samu girmamawa da kulawa ta musamman a NYSC camp saboda sunan Shagari da ya ke a maƙale da sunanshi, alhali shi ɗan talakawa ne a garin na Shagari. Wasu da yawa sun samu kulawa ta musamman a wuraren ɗaukar aikin gwamnati da na ɗamara daban-daban saboda sunan Shagari da ke maƙale a sunayensu. Wannan abu kuma zai ci gaba har abada matsawar akwai tarihi a ƙasar nan.

Hakan shi ya nuna cewa Alhaji Shehu Shagari ya samu sheda da karɓuwa da girmamawar da babu wani tsohon shugaban ƙasar nan ya samu a idon ƙabilu dabandaban a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya. Duk faaɗin ƙasar nan, duk da irin bambanci da rikicin addini da ƙabilancinta, babu inda za ka ambaci cewa Shehu Shagari mutumin kirki ne a ce maka “anya?”.

Babu wani lokaci da zan iya tuna Shugaba Shagari ya yi katsalandan ko nuna ɓangaranci a fili akan sha’anin mulki ko wani sha’anin siyasa na ƙasar nan da ma na jiharsa ta Sakkwato. Ya riƙe girman shi ya kuma kama mutuncin shi da har waɗansu su zata ya daɗe da mutuwa.

Rayuwa da mutuwar Shugaba Shagari sun zama wani babban darasi ga shuwagabbani kuma abin alfahari ga talakawan ƙasar nan. Kuma bai mutu ya bar ma zuri’a ko jihar shi abin kunyar da za a dinga jifar mu da shi ba.

Allah ya kai dausayin aljannah a makwancin Shehu Usman Aliyu Shagari.

The post Shehun Shagari, Shagarin Shehu – Mansur Isa Buhari appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here