Daga Mansur Ahmed

Da ya ke in ka yi magana a kan Buhari, yanzun nan za ka ga mahaukatan cikin masoyan sa sun fara zagin ka da cin zarafi sai ka d’auka Buharin ba shi ne wanda ya kasa yi wa Arewa komai ba ne. Yarabawa su na ta sharb’ar romon dimokaradiyya a kudanci, kai ka ce d’an su ne ke mulkin. Su kuwa mutanen Kano an bar su da ginin gidan yari, wanda shi ma ana yi ne saboda mummunar manufar Buhari ta tozarta ‘yan Arewa.

Ko da ya ke muna cikin jimamin karb’ar yankunan Baga da wasu manyan garuruwa da ‘yan Boko Haram su ka yi a cikin ‘yan kwanakin nan, da kuma rasuwar sojoji 126 da aka kashe kwanakin baya, ga shi kuma cikin satin da ya wuce an kashe sojoji 13 da d’an sanda d’aya ranar Talatar da ta gabata. ‘Yan agajin mu da aka yi garkuwa da su har yanzu babu labarin su, balle a samu shugaban k’asa ya jajanta wa kungiyar Izala ko ya yi magana domin a nemo su ruwa a jallo.

Kullum labarin irin na k’anzon kurege dai kawai a key i wa ‘yan Arewa farfaganda da shi – yau a ce Boko-haram ta k’are, gobe a ce sun tsere, jibi kuma a ce kad’an suka rage. Sai ka rasa labarin wanne ne na gaskiya? Abin da Buhari ya fi so shi ne a kawo malamai da ’yan wasan fim din Hausa da na yankin kudanci, a ci, a sha sannan ya fad’a musu ya na neman goyon bayan su game da komawar sa mulki.

A Jihar Zamfara rayukan mutane sun zama kamar rayuwar gandun dabbobi, ka je ka kama wanda ka ke so ka hallaka. A k’one inda ake so ko a yi garkuwa da wadanda ake so a nemi kudi mai tsoka da su. Idan ba’a biya ba a kashe ka kisan wulak’anci. Idan mace ce a yi ta fasik’anci da ita sai k’arfin ya k’are. Takaici da damuwa su saka ta kashe kanta ko su kashe ta bayan sun illatar da rayuwar ta. Wannan wacce irin masifa ce?

Abin d’aukar hankali da rainin wayon shi ne, gwamnan jihar Zamfara shi ne shugaban gwamnonin k’asar nan kullum yana tafe kamar an d’aura wa kare aure. Malaman mu da manyan Arewa sun kasa tsawatar masa ko shugaban k’asar ma ya kasa d’aukar mataki a kan sa, saboda ya na tsoron sa.

Wani abin takaici wai sai ka ji an ce Buhari ya kira Sarki wane a waya ya jajanta masa bisa abin da ya ke faruwa. Wannan ai ba ma abin fad’a ba ne domin nuna gazawa ce da halin ko in kula a kan rayuwar mutane. A banza Buhari ya ke zuwa taron murnar zagayowar haihuwar wani (birthday) ko k’addamar da littafi, amma ba zai iya zuwa ya nuna damuwa a kan talakan Arewa ba.

Garkuwa da mutane a Arewa ta zama kamar cin kasuwa. Ka na jimamin an kama wancan sai ka ji wancan ma ya shiga hannu. Abin da zai ba ka mamaki shi ne har yanzu ba’a d’auki wani babban mataki da zai bawa ‘yan k’asa k’warin gwiwar an kusa kawowa k’arshen matsalar ba. Nan aka kama wasu ’yan mata su biyu a Kebbi har da yayarsu da ’yan biyun suka fito shi kenan an wuce wajen. ’Yar uwar ta su ko a wanr yanayi ta ke? Oho!

Shi Buhari hankalin sa ya na kan yadda za’a yi ya koma mulki shi ya sa ba shi da lokacin da zai je Zamfara ja je, ko ya yi wuni biyu a can domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kan yadda za’a kawo k’arshen abin da ya ke faruwa. Amma zai iya zuwa taron wani aikin banza ko shan shayi a kan yanayi ko noman rani ko saka hannu a wata yarjejeniya a k’asashen k’etare. Tunda ya zama shugaban k’asa bai je Zamfara sau uku ba. Na tabbata an kashe ‘yan Nigeria sama da 500 a Zamfara amma yaje Ingila sau 8. Tsakanin Akwa Ibom da Zamfara wacce ta fi nisa? Buhari ya fi ganin zuwa Akwa Ibom saboda can kuri’a za’a samu Zamfara kuma rayukan mutane za’a kare. In a yankin Yarabawa a ke wannan abin da yanzu ka gan shi tunda su can ya fi tsoron su.

Nan wani d’an majalisa ya tashi a idon duniya ya bayyana wa duniya zahirin halin da ake ciki a jihohin Borno da Yobe game da abin da ke k’asa a kan Boko-haram. Amma mutane suka yi biris saboda ba’a son gaskiya, kuma hankalin shugabannin k’asar ya bar kan kare rayuka ya koma kan neman kuri’a.

Saura na ji wani shawaraki, dibgagge, gargajiga, salgoriyo ko makahon dan jagaliya ya fito ya zage ni. Wannan shine sak’o na na k’arshen shekara zuwa ga Muhammadu Buhari.

 

The post Tsakanin Buhari da ‘Yan Arewa: Kura da shan bugu. . . appeared first on Daily Nigerian Hausa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here