WAIWAYE ADON TAFIYA: Shekaru 6 na Zababben Gwamnan Jahar Jigawa, Muhammadu Badaru Abubakar – Mahmuda Yau Dan Sarki
“Akalan Gwamnatimmu zai karkata ne kacokam wajen harkar tsaro na rayuka da dukiyoyin al’umma, kazalika da harkar ilimi, wadacencen ruwan Sha, tsaftar muhalli da kiwon lafiya.
mataki na farko, samar da aikin yi ga matasa, karfafa guiwar mata wajen neman ilimi da dogoro da kai tare da yin nakasu ga talauci ta hanyar yin noma da sarrafa abinda aka girba, da cigaban rayuwar alumar Jahar da sauran bil Adama baki daya”.
Jawabin Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, MON, bayan rantsar da shi a shekarar 2015.
Maigima Gwamna Badaru, nada farin Jini ga al’umarsa kuma ya samu nasarori gaya bisa duk alkawarun da yayi wajen cigaban Jahar Jigawa da al’ummar Jahar dingurumdinsu.
Hakika, Gwamna Baduru Yana daga cikin jerin gwamnonin Tarayyar Najeriyya Masu kwazo, cancanta tare da yin aiki tukuru domin cigaban jahohinsu tare da kasa baki daya.
Gwamna Baduru ya aiwatar da muhimman ayyukan inganta rayuwar al’ummar Jahar Jigawa misali ta wajen fuskar, ilimi, harkar noma, kasuwanci da zuba hannun jari domin yin tasiri wajen habaka tattalin arzikin Jahar.
Gwamnatin Baduru ta yaye injinoyin aikin noma yayin data horas da matasa marasa aikin yi, sana’ar yin burodi tare da sauran aikace aikace irin na zamani.
Akwai kuma wadannan aka horas dasu aikin maganin ‘kwari da Masu girbi da shuka sama da mutum 2,000 da Masu sarrafa traktoci 60, Masu hadawa 20 da Masu kananan masussuka 500 da Masu fesa maganin kwari 2,500 yayin da an samarwa sama da mutum 5,000 gajiyar bashin karfafawa Kamar yadda ya Kamata wajen yin sana’a tare da aikin dogoro da kai.
Bugu da Kari, Gwamnatin Jahar Jigawa, karkashin jagoranci Gwamna Baduru tayi RAWAR GANI wajen tsaro yayin da gwamnatin ta turo jami’an maganin kwari 600 domin shawo kan wasu kwari da suka mamaye gonaki kusan jahohi goma 11 wajen kawad da kwari dake bata amfanin gona. Yayin da ma’aikatar JASCO ta cigaba da raba maganin kwari zuwa ga sauran wuraren da kwari suka addaba.
Read Also:
Shekaru Shidda da Gwamna Badaru yayi Yana mulki sunyi kicibis da kyawawan ayyuka a Jahar Jigawa, birni da kauyukan Jihar da karkara wajen raya Jihar tare da tabbatar da ayyukan cigaban more rayuwar al’ummar Jihar har da baki mazauna Jihar da ‘yan kasuwa da masu kawo ziyara ko zuba jari a Jahar.
Tuni kamfanin shinkafa na Dangote tare da kamfanin GNA na sigari ke cigaba da fadada hannun jarinsu ta fuskar harkar nomar shinkafa da harkar kasuwancin sikari a Jahar Jigawa.
Gwamnatin Badaru tayi alkawarin cigaba da hadin gwiwa da Masu hannun zuba jari da Yan kasuwa da masu kananan masanaantu wajen cigaba da inganta tattalin arzikin Jahar Jigawa yayin da Gwamnan ya rattaba hannun cimma wata yarjejeniya ta hadin guiwar tsakanin manoma da kasar Sin, China wajen harkar noman masara da shinkafa da kuma noman Rani a JaharJigawa.
Wani rahotan ma’aikatar kananan masana’antu ta SMEDAN ya bayyana cewa a shekarar 2013 akwai masana’antu matsakaita kanana sama da 820,001 a Jahar Jigawa daga cikinsu aka ware 1,022 a matsayin kanana yayin da 75 matsakaita.
Wannan ke nan ya nuna karancin matsakaita masana’antu a Jahar Jigawa da kuma rashin hadahadar kasuwancin na kananan yan kasuwa da kananan masana’antu.
Amma saboda jajircewar gwamnatin Baduru tare da hadin guiwa da hukumar bada jari ta Jahar Jigawa an samu habakar masana’antu da Albarkan arzikin karkashin kasa a Jihar yayin da tattalin arzikin Jahar na Kara bunkasa ta zuba jari a fanin kimiyya da fasaha tare da fadada kasuwar Jihar Jigawa ga Tarayyar Najeriya tare da sauran kasashen duniya baki daya.
Domin inganta harkar kasuwancin da hadahadar tattalin arziki, gwamnatin Baduru ta ware naira Milyan N300,000,000 wanda tuni an rabe su ga kamfanoni 95 wajen Fara yin aikin farko na farfado da tattalin arzikin Jahar Jigawa.
An samu nasarori matuka gaya cikin shekaru Shidda da Gwamna Badaru yayi Yana mulkin Jahar Jigawa, yayin da alumar Jahar Jigawa na cigaba da samun alhairai Masu Tarin Yawa sanadiyyar mulkin Gwamna Baduru da suka hada da tsarin kiwon lafiya, ilimi, ayyukan Yi ga matasa tare da tallafawa mata wajen gudanar da kananan masana’antu, ingantattun hanyoyin mota da asibitoci da sabbin makaratun firamare dana gaba da firamare har zuwa jami’a da sauran sassan guraben ‘karo ilimi masu zurfi na kimiyya da fasaha domin cigaban Jahar Jigawa.
Al’ummar Jahar Jigawa na son Barka da shekaru Shidda na mulkin Gwamna Baduru sabili da rayuwarsu ta samu cigaba da gaske daidai da kasashen da suka cigaba.
Marubuci: Mahmuda Yau Dan Sarki