Shigar Boko Haram: Gwamna Badaru ya Umurci Mutanen Jaharsa da Su Saka Ido a Kan Wanda ba su Yarda da Shi ba
Gwamna Muhammadu Badaru na jahar Jigawa ya ankarar da mutanen jaharsa game da yan Boko Haram.
Bayan taron tsaro da aka yi a gidan gwamnatin Jigawa, Badaru ya umurci mutane su kai wa jami’an tsaro rahoto kan duk wanda ba su yarda da shi ba.
Kwamishinan yan sandan Jigawa Usman Gomna ya shaidawa manema labarai cewa sun samu rahoton zargin yan Boko Haram sun shiga jahar kuma suna bincike.
Gwamnan jahar Jigawa, Muhammadu Badaru, a ranar Talata ya ankarar da mutanen jaharsa su rika saka ido kan abubuwan da ke faruwa a garuruwansu bayan rahotannin zargin yan Boko Haram sun fara shiga jahar Bauchi da ke makwabta da Jigawa.
A baya-bayan nan, gwamnatin jahar Bauchi ta sanar da cewa yan Boko Haram daga jahar Yobe sun shigo kananan hukumomi hudu a jahar wadda duk suna da iyakoki da Jigawa.
Read Also:
Sakataren gwamnatin jahar Bauchi, Sabiu Baba, yayin taron manema labarai a ranar Litinin ya ambaci wuraren da abin ya shafa kamar haka; Zaki, Gamawa, Darazo da Dambam.
Ya ce zargin ya yi karfi ne sakamakon yunkurin da aka yi na lalata na’urorin kamfanonin sadarwa a Gamawa.
Sakamakon abin da ya faru a Bauchi da ke makwabtaka da Jigawa ya saka Gwamna Badaru ya yi taro da masu sarautun gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da hukumomin tsaro a dakin taro da ke gidan gwamnati inda a karshe he bukaci mazauna garin su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba.
“Batun tsaro a kasar nan yasa aka kira taron. Muna ganin ya kamata kowa ya zage damtse ya saka ido sannan mu yi addu’ar Allah ya tsare kasarmu da Jigawa,” in ji Badaru.
Kwamishinan yan sandan jahar, Usman Gomna ya shaidawa manema labarai cewa sun samu bayannan sirri kan wasu da ake zargin yan Boko Haram ne a Gwaram kuma suna bibiyan lamarin.