Shirin da Batagari Suke Son yi da Bikin Kirismeti

 

Ana shirin kai hari coci-coci lokacin bikin Kirismeti da sabuwar shekara.

Kakakin DSS, Afunanya, ya ankarar da yan Najeriya, musamman masu bukukuwa.

Ya bukaci yan Najeriya su nisanci taron jama’a musamman wannan lokacin.

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta gano wani shiri da wasu bata gari ke yi na sanya Bam a wuraren da ke da taron jama’a a fadin kasar lokacin bikin Kirismeti da sabon shekara.

A jawabin da kakakin hukumar, Peter Afunanya, ya saki ranar Talata, ya yi kira ga yan Najeriya su farga, kuma su fadawa jami’an tsaro duk wani abinda suka gani basu yarda da shi ba.

“Hukumar DSS na sanar da daukacin jama’a shirin da wasu batagari ke yi na kai hare-hare wuraren dake da taron jama’a wanda ya hada da manyan wurare lokacin hutun Kirismeti da sabon shekara,” wani sashen jawbai yace.

“An yi shirin kai wadannan hare-hare ne ta hanyar amfani da bama-bamai, masu kunar bakin wake da kuma wasu makamai masu hadari.”

“Manufar haka shine saka tsoro cikin zukatan mutane da kuma bata sunan gwamnati.”

“Saboda haka, yan Najeriya su kasance cikin farga kuma su bada rahoton duk wani abin da suke zargi ga hukumomin tsaro.”

Hukumar tana baiwa yan Najeriya tabbacin cewa tana hada kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyan al’umma.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here