Shehu Sani ya yi wa Gwamnan Kano Martani

Shehu Sani ya soki wata doka da Gwamnatin Jihar Kano ta kawo.

An hana duk masu manyan motoci ajiye fasinjojinsu a Sabon Gari.

Tsohon Sanatan ya roki Gwamnatin Kano ta janye wannan dokar.

Sanata Shehu ya yi magana game da sabon tsarin da gwamnatin jihar Kano ta kawo, wanda masu harkar manyan motoci su ke kuka da shi.

Kwanaki Gwamnatin jihar Kano ta sa masu tuka manyan motoci su bar tashar Sabon Gari, su koma ajiye fasinjojinsu a hanyar Maiduguri.

Shehu Sani ya bayyana cewa wannan doka da Mai girma Dr. Abdullahi Ganduje ya kawo ta sabawa dokar kasa, don haka ya nemi a soke ta.

Ga abin da Sanata Sani ya rubuta a shafinsa na Twitter:

“Ya gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ka janye matakin da ka dauka na canzawa masu harkar manyan motoci wuri na daina sauke fasinjoji a tashar Sabon Gari, su koma babban hanyar zuwa garin Maiduguri.”

Tsohon ‘dan majalisar dattawan ya kuma roki gwamnatin Kano ta cire harajin Naira miliyan 10 da ake rade-radin za a rika karba kan masu saba dokar.

Ya ce: “Idan sauran jihohi su ka fara yin haka, an yi watsi da dokar da ta halatta zirga-zirga.”

Kawo yanzu gwamnatin Abdullahi Ganduje ba ta maida martani ba, kuma babu sanarwar an janye wannan dokar lodi ko kuma harajin da aka shigo da shi.

Tuni dai kungiyar ALBON ta masu manyan motoci su ka nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan shi ya tsoma baki game da dokar da aka kawo.

Masu aikin manyan motoci sun ce wannan doka da aka kawo ta na wahalar da su a wajen aiki, a lokacin da ‘yan kasuwa ke neman agajin gwamnatin kasar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here