Shirin Nukiliya: Babban jami’in EU Zai Ziyarci Tehran
A wannan Alhamis din ne babban mai sanya ido na tarayyar turai kan Iran zai ziyarci Tehran, don roƙon ƙasar ta sake shiga tattaunawa a Vienna kan shirinta na nukiliya.
Enrique Mora yana fatan gamsar da Iran don ci gaba da tattaunawa da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliya ta 2015.
Iran ta fasa tattaunawar watanni hudu da suka gabata.
Ziyarar ta Mora na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka da Isra’ila suka ce suna duba wasu hanyoyi na daban na diflomasiyya idan Iran ta ƙi yadda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya ce lokaci ya kure kuma Amurka za ta duba kowane zabi.