Shugaba Bah Ndaw da Firam Ministansa Sunyi Murabus Daga Kujerunsu

Shugaba Bah Ndaw da Firam Ministansa Sunyi Murabus Daga Kujerunsu

Shugaban kasar Mali da Firam Minista sun yi murabus daga kujerunsu bayan tsaresu da Sojoji sukayi ranar Litinin, wani hadimin sabon shugaban na yanzu bayyana.

Shugaba Bah Ndaw da Firam Ministansa Moctar Oaune sun yi murabus gaban Alkalai,” Baba Cissé, mamban kwamitin sulhu da aka tura wanda kuma hadimi ne ga Kanal Assimi Goïta yace.

“Ana cigaba da tattaunawa domin sakesu da kuma kafa sabuwar gwamnati,” ya kara.

Wani mamban kwamitin sulhun na daban wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyanawa AFP cewa lallai da gaske Bah ya yi murabus.

Wata tawagar gamayyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta dira inda aka tsare shugaban lasan da Firai Ministansa a barikin Kati, ranar Laraba domin ganin halin da suke ciki.

Kanal Goïta, wanda shine mataimakin shugaban kasa ya tuhumci Bah Ndaw da Oaune da kin damawa da shi wajen wasu sauye-sauye.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here