Ko za a Cire Tallafin Man Fetur, ko ba za a Cire ba, ya Kamata Farashin Mai ya Canza – Shugaban Kungiyar MAN

Shugaban kungiyar MAN ya na ganin babu makawa kan tashin farashin fetur.

Segun Ajayi-Kadir ya ce a yau danyen mai ya kara kudi a kasuwannin Duniya.

Matsalar rashin matatu zai taimaka wajen tsadar fetur a gidajen man Najeriya.

Kungiyar MAN ta masu kere-kere a Najeriya, ta na ganin ya wajaba a samu sauyi a farashin fetur.

A ranar Laraba, 26 ga watan Mayu, 2021, jaridar Punch ta rahoto MAN ta na cewa babu makawa, sai an yi karin kudin litar man fetur a kasar nan.

Darekta Janar na kungiyar MAN na kasa, Segun Ajayi-Kadir, ya ce ko za a cire tallafin man fetur, ko ba za a cire ba, ya kamata farashin mai ya canza.

Segun Ajayi-Kadir yake cewa bai kamata a rike farashin lita ba, ya bukaci hukuma ta kyale farashin ya rika yawo a kasuwa gwargwadon bukata.

Shugaban MAN, Ajayi-Kadir, ya bayyana wannan ne a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida, bayan gwamnoni sun bada shawarar kara farashi zuwa N385.

Ya ce: “Ya kamata tashin danyen mai ya yi tasiri a kudin litar man fetur a kasar nan, musamman a lokacin da matatun manmu ba su aiki yadda ya dace.”

“Bayan haka, gwamnati ta na ta faman cigaba da biyan kudin tallafin man fetur.” Inji Ajayi-Kadir.

“Muna da ‘yan kasuwa da ke kutsa kai a harkar shigo da mai, wanda suke bukatar suyi kasuwanci, su samu riba, la’akari da haka, dole farashi ya karu.”

Amma duk da wannan hasashe da kungiyar ta ke yi, Ajayi-Kadir ya na ganin tsaida farashin lita a kan N385, zai taba tattalin arziki ta mummunar hanya.

Brandspurng ta ce MAN ta na ganin wannan kari zai jawo kudin mota ya kara tsada a Najeriya, sannan za a samu karin tsadar rayuwa, ga karancin kudi a hannu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here