‘Yan Bindiga Sun kai Hari Jahar Delta Sun ƙona Motar Sintirin ‘Yan  Sanda, Sun Kashe Jami’i ɗaya

 

Wasu yan bindiga sun hallaka ɗan sanda guda ɗaya, sun ƙona motar sintirin yan sanda a jahar Delta

Kakakin hukumar yan sanda na jahar, Edafe Bright, ya tabbatar da kai harin, amma yace har yanzun suna gudanar da bincike

Yace an kai wa jami’an yan sanda hari a ƙauyen Akwukwu Igbo, amma an samu nasarar damƙe shugaban maharan

An hallaka wani ɗan sanda ɗaya tare da ƙona motar sintiri a wani sabon hari da yan bindiga suka kai ƙaramar hukumar Aniocha dake jahar Delta, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kakakin hukunar yan sandan jahar, Edafe Bright, ya tabbatar wa dailytrust da faruwar lamarin, amma yace an kama wasu daga cikin maharan.

Yace: “Eh, an kaiwa jami’an mu hari da misalin ƙarfe 6:20 na safiyar yau Laraba a ƙauyen Akwukwu Igbo. Ɗaya daga cikin jami’an mu ya rasa ransa sannan sun ƙona motar sintiri.”

“Amma mun samu nasarar damƙe shugaban waɗanda suka kawo harin, a halin yanzun muna cigaba da bincike.”

Edafe ya ƙara bayyana cewa rundunar yan sanda na cigaba ƙoƙari domin ganin an kamo sauran mutanen da suka gudu.

Ana cigaba da samun ƙaruwar kai hare-hare ga jami’an hukumar yan sanda a yankin kudancin ƙasar nan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here