Jahohi ne ya Kamata su Yanke Kwatankwacin Yawan Kananan Hukumomin da Zasu Iya ɗauka – Gwamna El-Rufa’i

 

Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i, yace kamata yayi a baiwa gwamnonin jahohi damar yanke yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka.

Gwamnan yace idan akace za’a maƙala wa gwamnatin tarayya dukka ƙananan hukumomin ƙasar nan to an saɓawa tsarin mulkin jamhuriya.

El-Rufa’i ya faɗi haka ne a wajen ji ta bakin jama’a akan kudirin gyara kundin tsarin mulkin ƙasar nan da yan majalisa suka shirya

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, yace jahohi ne ya kamata su yanke kwatankwacin yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka.

Gwamnan yace Najeriya ƙasa ce dake ɗauke da gwamnatocin jahohi 36 da kuma gwamnatin tarayya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A cewar gwamnan, a lissafo jerin kananan hukumomin ƙasar nan 774 sannan ace ana son maƙala wa gwamnatin tarayya su kai tsaye, wannan ya saɓa wa tsarin mulkin da muke tafiya a kanshi na jamhuriya.

El-Rufa’i yayi wannan jawabi ne a wurin jin ta bakin al’umma kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan a ranar Laraba.

El-Rufa’i yace “Kamata yayi a bar kowace jaha ta yanke adadin yawan ƙananan hukumomin ta waɗanda zata iya samar wa kuɗaɗe kwatankwacin kuɗin shigarta, hakan zai sa a gudanar da gwamnati mai kyau kuma cikin adalci.”

“Kowace jaha ita ya kamata ta duba ta ga tsarin yadda take son kananan hukumominta su kasan ce, amma dai abunda ake so shine a sanya tsarin demokaraɗiyya a cikin kowane tsari.”

“Kuma a baiwa kowace jaha lokacin gudanar da zaɓen ƙananan hukumominta amma kar ya wuce tsawon shekaru huɗu a tsakani.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here