Yadda Shugaba Buhari ya Siffanta Cutar Corona

 

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akwai bukatar hadin kai don yaki da Korona.

Shugaban ya siffanta Korona da wani kalubale dake addabar duniya kamar sauran ta’addanci.

Shugaban ya bukaci kasashe da su hada kai don samun mafita kan yaduwar Korona.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake jaddada bukatar kasashen duniya su hada kai tare wajen tunkarar cutar COVID-19 kamar sauran kalubalen da ke addabar duniya, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake jawabi a wajen taron karbar takardun wasikar amincewa da sabbin jakadun Masar, Saudi Arabia da Argentina a fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Alhamis, shugaban ya bayyana cewa:

“Muna da kalubale iri daya da ke tasiri sosai ga kasashenmu, wadanda suka hada da ta’addanci, tayar da kayar baya, canjin yanayi, fashewar jama’a, safarar mutane, rashawa, talauci, da kuma yaduwar kananan makamai.

“A saman wadannan duka, zango na biyu na annobar COVID-19 ya zo da iri daban-daban da ke haifar da karin kalubale ga bullowar farko.

Shugaba Buhari ya kuma nuna matukar farin cikinsa ga hadin kan da Najeriya da sauran kasashen uku suka samu a wasu fannoni.

“Duk kasashe ukun da aka wakilta a nan suna da kyakkyawar dangantakar bangarori tare da mu. Jakadun, wadanda suka gabatar da wasikun amincewarsu, su ne:

Mista Ihab Moustafa Awad Moustafa daga Jamhuriyar Larabawa ta Masar, Mista Faisal Ebraheem Alajrafi Alghamdi daga Masarautar Saudiyya, da Mista Alejandro Miguel Francisco Herrero daga Jamhuriyar Argentina.

Shugaban ya nanata wa Jakadun shirin na Najeriya “don yin aiki tare da ku baki daya don samun zaman lafiya a duniya, wadatar abinci da muhalli mai dorewa.”

Yayin da yake yi wa manzannin fatan alheri a wa’adinsu, ya yi musu fatan su fadada matsayin da suke a yanzu.

“Za mu dogara da irin taimakon da kuke bayarwa da kuma jagora har zuwa wannan,” in ji Mista Moustapha.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here