Da Gaske Ganyen Wiwi Yana Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Yakar Cutar Corona ?

Masana sun nuna fa’idar ganyen wiwi wajen yakar Coronavirus.

An gudanar da wani bincike a kasar Kanada da ya nuna wannan.

COVID-19 ta hallaka mutane fiye da miliyan 2 a kasashen Duniya Wani sabon nazari da aka gudanar da ganyen wiwi ya nuna tabar za ta iya taimaka wa jiki daga Coronavirus ta hanyar kumbura gabban numfashi.

Jami’o’in Calgary da na Lethbridge da ke kasar Kanada ne su ka gudanar da wannan bincike tare da hadin-gwiwar masu bincike na Pathway Research Inc.

Jaridar Punch ta ce an wallafa sakamakon wannan nazarin kimiyya a mujallar kiwon lafiya Aging.

Wadanda suka gudanar da binciken sun ce ana samun girgizar da ake kira cytokine storms a lokacin da mutum ya fitar da kwayoyin halittar kariya sosai.

Wannan girgiza ta kan jawo mummunan hawan jini, da matsala a hunhu wanda ke kai wa matsalar numfashi a jikin mutum, kamar yadda binciken ya nuna.

Wasu mutanen su kan samu damar yaki da COVID-19 a duk lokacin da jikinsu ya rika fitar da kwayoyin garkuwa da yawa wadanda za su yaki kwayar cutar.

Nazarin da aka gudanar ya nuna mutanen da su ka mutu a sakamakon girgizar da suka samu sun fi wadanda ainihin cutar murar mashakon ta hallaka yawa.

Daya daga cikin wadanda su ka yi wannan bincike, Dr. Igor Kovalchuk na jami’ar Lethbridge da ke garin Alberta, ya ce sam bai yi mamakin abin da suka gani ba.

Har a jikin dabbobi, wiwi ya kan rage daskarewar jini, wannan ya na da tasiri ga cutar COVID-19.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here