Shugaban Karamar Hukuma a Jihar Anambra ya Shiga Hannu Kan Mutuwar Matarsa

 

Mbazulike Iloka, shugaban karamar hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Anambra yanzu yana hannun yan sanda.

Yan sanda sun kama Iloka ne a ranar Laraba 17 ga watan Agusta, kan zarginsa da hannu a mutuwar matarsa.

Amma, mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar, Ikenga Tochukwu, ya ce sashin SCID har yanzu suna bincike.

Nnewi ta Arewa, Anambra – Mbazulike Iloka, dakataccen shugaban kwamitin mika mulki na karamar hukumar Nnewi ta Arewa a Jihar Anambra, ya shiga hannun yan sanda a jihar kan zarginsa da hannu kan mutuwar matarsa.

Kakakin yan sandan Jihar, Ikenga Tochukwu, wanda ya yi magana da yan jarida a ranar Laraba 17 ga watan Agusta ya tabbatar da kama Iloka, The Nation ta rahoto.

Tochukwu ya bayyana cewa an kama Iloka ne kan zargin yana da hannu a mutuwarsa, Chidiebere.

Amma, jami’in mai magana da yawun yan sandan ya ce, sashin binciken manyan laifuka na rundunar, SCID, har yanzu tana bincike kan abin da ya faru.

Wani rahoto da Punch ta wallafa ya rahoto an jiyo yana cewa:

“Yana hannun mu kuma muna rokon al’umma su yi hakuri saboda binciken sanadin rasuwa da likitoci ke yi zai bayyana abin da ya halaka matar. A halin yanzu, ana cigaba da bincike.”

Yadda matata ta mutu – dakataccen shugaban karamar hukumar ya magantu

Idan za a iya tunawa Iloka ya yi martani kan dakatar da shi kan mutuwar matarsa.

Ya bada bayanin yadda matarsa ta rasu. Dan siyasan, ya yi ikirarin cewa mutane a dandalin sada zumunta, saboda wani bidiyon gawar matar suna ikirarin cewa azaba da ta ke sha a gidan miji ne ya yi sanadin mutuwarta, abin da ya ce ba gaskiya bane.

Ya dage cewa Chidiebere ta rasu ne saboda wani mummunan fadi da ta yi amma ba dukkanta ya ke yi ba.

Mbazulike ya kara da cewa akwai shaidu a wurin a lokacin da abin ya faru kuma ya yi kira ga al’umma su dena yadda jita-jita na cewa dukanta ya ke yi amma su yi mata addu’a da iyalanta.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here