Bincike: A Cikin N431m da Magu ya Handame ya yi Amfani da Kudin Don Biyan Wutar Lantarkin Gidan Gonarsa

 

Kwamitin Mai Shari’a Ayo Salami ya bankado yadda Ibrahim Magu, dakataccen shugaban EFCC ya handama daga cikin N431 miliyan ya biya wutar lantarkin gidan gonarsa.

Kamar yadda rahoton binciken Magun da aka mika ofishin sakataren tarayya ya bayyana, ya kwasa daga kudin inda ya biya kudin kallon talabijin na gidansa dake Karu.

A yayin da aka tuntubi lauyan Ibrahim Magu, ya ki tofa albarkacin bakinsa kan zancen inda yace har a halin yanzu bai samu ganin takardun binciken da kwamitin Salami yayi ba.

FCT, Abuja – Kwamitin bincikar Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da almundahana da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, EFCC, yace ba zai iya bayyana yadda aka kashe N431 miliyan ba na tsaro da aka warewa ofishin Magu ba tsakanin 2015 zuwa 2020.

A rahoton karshe da aka mikawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Nuwamban 2020, an gano cewa Magu yayi amfani da wasu daga cikin kudin wurin biyan kudin wutan gonarsa dake Karshi Development Area dake Nasarawa, TheCable ta rahoto.

Kwamitin ya kara da cewa, tsohon shugaban EFCC yayi amfani da wani bangare na kudin wurin biyan kudin kallon talabijin na gidansa dake yankin Karu a jihar.

Kwamitin da ya samu shugabancin Ayo Salami, tsohon babban alkalin kotun daukaka kara, an kafa shi ne domin binciken Magu tun daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2020, lokacin da ya mulki hukumar.

TheCable ta gano an mika rahoton zuwa ofishin sakataren gwamnatin tarayya. Lokacin da TheCable ta tuntubi lauyan Magu, Wahab Shittu domin yayi martani kan lamarin, ya ki cewa komai saboda yace bai ga takardun ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here