Kwankwaso ya yi Karin Haske Kan Jita-Jitar Ficewar Shekarau Daga NNPP

 

Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce tsakaninsa da mutanen Sanata Ibrahim Shekarau babu wata rigima.

‘Dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar NNPP ya shaidawa ‘yan jarida haka a wata hira da ya yi.

Ana rade-radin tsohon gwamnan Kano watau Ibrahim Shekarau zai fice daga NNPP bayan kwanaki.

Abuja – Rabi’u Musa Kwankwaso ya shaidawa Duniya cewa a halin yanzu babu wata rigima da ake yi tsakaninsa da tsaginsu Malam Ibrahim Shekarau.

A ranar Laraba, 17 ga watan Agusta 2022, BBC Hausa ta zanta da Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya yi karin haske a kan tafiyar jam’iyyar NNPP.

Rabiu Kwankwaso ya yi watsi da rade-radin da ake yi cewa babu zaman lafiya a NNPP tsakanin mutanensa da kuma ‘yan bangaren Sardaunan Kano.

Jita-jitar rabuwar kai da barazanar barin NNPP da su Shekarau suke yi ya je kunnen Kwankwaso, wanda ya shaida cewa ba haka gaskiyar lamarin yake ba.

An saba yarjejeniya da Shekarau?

‘Dan siyasar ya fadawa BBC cewa ba a kulla wasu yarjejeniya wajen jawo Malam Shekarau zuwa NNPP ba, sai dai ya ce akwai bukatun da aka gabatar.

Kamar yadda jagoran na NNPP na kasa ya fada, bangaren Sanatan na Kano ta tsakiya ba su gabatar da bukatunsu a kan kari, a lokacin da ya dace ba.

‘Dan takarar shugaban kasar a inuwar NNPP yace an yi bakin kokarin biyawa bangaren Sanata Shekarau bukatun tsayawa takara, amma lokaci ya matse, Saboda akwai wa’adin da hukumar zabe ta bada domin kammala tsaida gwani, ba duka bukatun su Shekarau ne jam’iyyar NNPP ta iya biya masu a Kano ba.

Hakan ba zai yi tasiri a NNPP ba Kwankwaso yace wannan matsala da aka samu ba za ta taba alakar da ke tsakaninsa da Shekarau ba.

Sahelian Times ta fitar da irin wannan rahoton.

Sanata Kwankwaso ya yi alkawarin idan NNPP ta karbi gwamnati, za a warewa mutanen da ke tare da tsohon abokin adawarsa mukamai masu tsoka.

Wasu daga cikin ‘yan tsagin Malam Shekarau su na kukan an yi watsi da su a tafiyar NNPP a Kano, sun ce ‘Yan Kwankwasiyya ne kadai ake damawa da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here