Shugaban Hukumar FRSC, Boboye Oyeyemi ya yi Ritaya Daga Aiki

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa watau Federal Road Safety Comission (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya yi ritaya daga aiki.

Boboye Oyeyemi yana daya daga cikin tsirarun jami’an da suka kafa hukumar Federal Road Safety Comission FRSC a Najeriya.

Oyeyemi yayi Ritaya shekaru takwas bayan da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi a matsayin shugaban FRSC.

ABUJA – Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa Federal Road Safety Comission (FRSC), Boboye Oyeyemi, ya yi ritaya daga aiki. Rahoton INDEPENDENT

Ranar Juma’a 19 Yuni za a mishi Faretin fita daga aiki (Pull Out Parade) a Abuja kafin a sanar da wanda zai maye gurbin sa.

Oyeyemi yayi ritaya shekaru takwas bayan da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya nada shi a matsayin Corps Marshal a ranar 23 ga Yuli, 2014.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in kula da hulda da jama’a na hukumar Federal Road Safety Comission, FRSC Bisi Kazeem ya fitar.

Oyeyemi wanda yana daya daga cikin tsirarun jami’an da suka kafa hukumar Federal Road Safety Comission FRSC, ya yi aiki a dukkanin manyan ma’aikatun hukumar, kuma ya yi fice wajen gudanar da aikin sa yadda ya kamata.

Cikin kudurin sa Oyeyemi Boboye, ya magance matsalar rashin matsuguni na ofis wanda yawancin jihohi haya hukumar take yi. Ya tabbatar da an gina ofis na din-din a duka shiyoyin kasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here