Zaben Osun ya Nuna Mana Cewa Akwai Aiki a Gabanmu – Shugaban Jam’iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah.

Abdullahi Adamu ya ce ba rashin iya siyasa bane ya janyo APC ta fadi a zaben gwamnan jihar Osun.

Jam’iyyar APC ta yi kira ga mambobinta da su gyara kurakuran su gabanin babban zabe mai zuwa a 2023.

Abuja – Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Senata Abdullahi Adamu, ya ce faduwar APC a zaben gwamnan jihar Osun jarrrabawa ce daga Allah. Rahoton BBC

Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da BBC HAUSA, inda yace

“Ya zama dole mambobin jam’iyyar APC su gyara kurakuran su gabanin zaben shugaban kasa na 2022.

“Zaben Osun ya nuna mana cewa akwai aiki a gabanmu, dole ne mu gyara abubuwan da mu ke yi ba daidai ba.

“Kuma faɗuwar APC a jihar Osun ba ita ce ke nufin jam’iyyar za ta faɗi a babban zaɓen dake zuwa 2023 ba.

A cewarsa jam’iyyar za ta duba abubuwan da suka janyo APC ta faɗi zaɓen jihar Osun domin gyara saboda samun nasara a zaɓen ƙasa mai zuwa.

“Harkar siyasa kamar sauran harkokin rayuwa ne, wata rana ka samu wata rana kuma ka rasa. Iko ne na Allah, babu yadda muka iya dole mu dauki kaddara.

Abdullahi Adamu ya ce ba an kayar da APC bane saboda rashin iya siyasa, sai dai matsalolin dake tsakanin ‘yayan jam’iyyar gabanin zaɓen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here