Shugaban Kasar Kamaru na Bikin Shekara 90 da Haihuwa
A yau ne Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya, yake bikin cikarsa shekara 90 da haihuwa, a matsayin shugaban kasar da ya fi dadewa a duniya a yanzu.
An haifi shugaban wanda ya kama mulki a 1982 a shekarar a kauyen Mvomeka’a, da ke kudancin kasar a 1933.
Read Also:
Rahotanni na cewa gazawarsa ta inganta rayuwar ‘yan kasar da kuma tashin hankalin da ‘yan aware na yankin da ke amfani da Turancin Ingilishi ke yi sun dusashe karsashin da gwamnatinsa ta samu a farko-farkon hawansa mulki.
Ba sosai ake ganin shugaban yanzu a bainar jama’a ba kuma ana ganin ma yana zama yawanci a kasashen waje ne
Shekara biyu da ta gabata, sakamakon dadewa da ya yi ba a gan shi ba aka rika yada jita-jitar mutuwarsa a sanadiyyar Korona.
Shugabannin ‘yan hamayya suna ta kira gare shi da ya sauka daga mulki, yayin da magoya bayansa ke cewa ya ci gaba da cewa shugabanci sai dattijo.